An Koma tattunawa Tsakanin Tawagar Iran Da Ta Kasashen Turai Kan Cire Mata Takunkumi.
Ali Bagheri Khan babban mai shiga tsakani na kasar Iran ya isa birnin Vienna tuna jiya talata domin ci gaba da tattaunawa zaga ye na 8 tsakaninsu da kasahen turai guda biyar, don cire mata takunkumi,
kuma tuni ya fara ganawa da Enrique Mora mai kula da siyasar waje na kungiyar tarayyar Turai wato EU, kuma ana saran zai gana da sauran jagororin tawagoginmahalarta taron.
Bayan kwashe mako guda ana tuntubar juna ta diplomasiya , tattaunawa zagaye na 8 ta cirewa Iran haramtaccen Takunkumi ta fara aiki, wanda aka fara tun aranar 27 ga watan Decembar day a gabata, bayan takaitaccen hutu a koma aiki a ranar 7 ga watan Fabareru da muke ciki.
Tuni iran ta sha nanata cewa duk da cewa Amurka ta keta hurumin yarjejeniyar da aka cimma ta JCPOA , ya zama wajibi ta dawo cikin tattaunawar tare da dauke dukkan takunkkumi da bashi da halarci da ta sanyawa Iran, kuma ta cika dukkan Alkawuran da ta dauke a yarjejeniyar.
A baya bayan nan ne dai Amurka ta sanar da janye takunkumin da ta sanyawa Iran kan shirin nukiliyar ta na zaman lafiya a matsayin wanimataki na nuna kyakkawar aniya na dawowa cikin yarjejeniayr da aka cimma a shekara ta 2015 lamarin da iran ta bayyana shi a matsayin na fatar baki kawai don har yanzu bata gani a rubuce ba.