Yakin Gaza ya shiga wata na 11, inda dubun dubatar mutane suka mutu, kuma kokarin da kasashen duniya ke yi na shiga tsakani a tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ya ci tura, yayin da suke zargin juna da yin karin wasu bukatu da ba za a amince da su ba.
Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza cikin dare da kuma a ranar Larabar da ta gabata sun kai hari makarantar Majalisar Dinkin Duniya da ke matsugunin iyalan Falasdinawa da ma wasu gidaje biyu, inda suka kashe akalla mutane 34 da suka hada da mata da kananan yara 19.
Yakin Gaza ya shiga wata na 11, inda dubun dubatar mutane suka mutu, kuma kokarin da kasashen duniya ke yi na shiga tsakani a tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ya ci tura yayin da suke zargin juna da yin karin wasu bukatu da ba za a amince da su ba.
A yankin yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, sojojin Isra’ila sun kaddamar da hare-hare a wasu garuruwa da ke samun goyon bayan jiragen sama, inda suka ci gaba da kai hare-hare a fadin yankin da sojojin suka ce suna auna ‘yan ta’adda amma sun lalata unguwanni tare da kashe fararen hula.
Wani harin da aka kai ta sama ya kashe mutane biyar da sojojin suka ce mayakan da ke yi wa dakarun nata barazana. Wani hari na biyu da aka kai kan wata mota ya kashe akalla mutane uku, in ji ma’aikatar lafiya ta Falasdinu.
Wani maharin ya afkawa wata motar man fetur a wata tashar bas ta gabar yammacin kogin Jordan kusa da matsugunan Isra’ila na GIvat Assaf, inda ya kashe wani sojan Isra’ila, in ji rundunar sojin. Jami’ai sun ce sojoji da wani farar hula dauke da makamai sun “tsare” maharin.