Matashi ya mutu sanadiyyar gardamar kwallon kafa ta turawa a Katsina
Gardamar kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Chelsea ta yi sanadiyyar mutuwar wani matashi a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina.
Kamar yadda Katsina Post ta samu labari, gardamar kwallon kafa ce ta kaure a tsakanin matasan biyu kafin daga bisani daya daga cikin su mai suna Idris Yusuf dan shekara 18 ya kashe dayan abokin gardamar ta shi mai suna Saifullahi Abdullahi mai shekaru 28 a duniya.
Haka zalika kamar yadda muka tabbatar, lamarin wanda ya auku tun cikin watan Disemba din shekarar 2021 yanzu haka kes din na gaban alkali a wata kotun Majistare a garin Katsina.
A zaman kotun da ya wakana a ranar Litinin, Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida ma kotun cewa mahaifin Marigayi Saifullahi ne ya kai kara a ofishin yan sandan garin na Danja lokacin da lamarin ya auku.
Dan sandan, Sajan Lawal Bello ya kara da cewa mamacin ya rasu ne sanadiyyar rigimar da ta kaure tsakanin sa da wanda ake tuhuma wanda ya yanke jiki ya fadi kafin daga bisani ya rasa ran sa a wata asibiti.
Alkaliyar kotun, Mai Shari’a Fadila Dikko ta sa ranar 7 ga watan Maris domin cigaba da shari’ar kuma ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali har lokacin da za’a cigaba dad shari’ar.
Labari daga Katsina post.