An Kashe Gwamman Sojojin Kasar Siriya A Wani Harin Ta’adanci Da Aka Kai A Birnin Homa.
Kamfannin dillancin labaran kasar Siriya SANA ya nakalto cewa akalla an kashe sojojin kasar guda 13 tare da jikkata wasu da dama sakamakon hari da kungiyar Ta’adda ta Takfiri dake samun goyon bayan kasashen wajen ta kai kan motar Bus da suke ciki a kan hanyarsu ta zuwa garin Homa dake lardin tsakiya.
Lamarin ya faru ne da yammacin jiya lahadi inda yan ta’addan suka auna motar bus da sojojin suke ciki da muggan makamai a gefen garin Palmyra dake gabashin Badiya.
Da yawa daga cikin mambobin kungiyar Daesh da aka kama sun yi Ikirarin yin aiki tare da sojojin Amurka a sansanins dake Al-Tanf domin kai hare hare da yin zagon kasa a kasar ta siriya.
A wata hira da gidan talabijin din kasar yayi da wasu daga cikin yan ta’adda da aka kama sun bayyana cewa sun samu umurni ne daga sojojin Amurka na su kai hari kan tawagar sojojin kasar Siriya , inda agefen garin Palmyra akwai sansanin soji a wajen dake da albarkatun iskar gas da rijiyoyin manfetur a wajen ,
Kasar Siriya ta samu nasarar fatattakar dakarun kungiyoyin yan ta’adda a yankuna daban daban na kasar, sai dai har yanzu sauran gyauransu suna kai hare haren sari ka noke a wasu yankunan masu nisa a kasar.