An Kasa Cimma Matsaya A Tattaunawar Sulhu Da Aka yi Zagaye Na 3 Tsakanin Rasha Da Ukrain.
Rahotanni sun bayyana cewa An kammala tattaunawar sulhu tsakanin kasashen Rasha da Ukrani batare da kulla wani abin azo a gani ba, sai dai jami’an gwamantin kasar Ukrain sun nuna cewa an samu canji kadan game da hanyoyin da za’a bi wajen kare fararen hula
Zagayen farko na tattaunawar an yi ta ne a birnin Gomle na kasar Belarus a ranar 28 ga watan Fabareru , sai na biyu kuma an shi ya ne a ranar 3 ga watan maris a garin Brest Bloer dake kusa da iyaka,
Sai dai ya zuwa yanzu bbau wani ci gaba da aka samu , a nasa bangaren mai shiga tsakani na kasar Ukrain a tattaunawar ya wallafa a shafinsa na twiter bayan tattaunawar cewa akwai wani ci gaba kadan da aka samu day a shafi kare rayukan fararen hula, sai dai bangarorin biyu za su ci gaba da tattaunawar game da batu tsagaita bude wuta.
A nasa bangaren mai shiga tsakani na kasa Rasha Viladmir Madinsky ya fadi cewa yana fatan batun bude hanyoyin kare fararen hula a kasar Ukrain zai fara aiki a yau talata, sai dai babu abin da aka cimma a bangaren siyasa, sai dai akwai kyakkyawar tattaunawar ta gaba za ta haifar dad a mai ido