Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta bayyana cewa, an matsa kaimi irinsa na farko a tarihi wajen yaki da matsalar sauyin yanayi a daidai lokacin da kasashen duniya kimanin 200 suka gudanar da taro tare da amincewa da wani rahoton kwararru domin magance matsalar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar wasu tarin matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi kamar bacewar wasu nau’ukan halittu daga doran-kasa da lalacewar zamantakewa tsakanin tsirrai da muhalli da tsanantar cutakan da sauro ke yadawa da tsananin zafi da karancin ruwa baya ga kankancewar albarkatun gona.
A bara kadai, duniya ta gamu da jerin musibun ambaliyar ruwa mafi muni a tarihi, gami da matsanancin zafi da barkewar wutar daji a nahiyoyi hudu na duniya.
Rahoton kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, dukkanin matsalolin da sauyin yanayin ya haddasa, za su ta’azzara nan da wasu gomman shekaru masu zuwa, koda kuwa an shawo kan matsalar hayaki mai gurbata muhalli.
Nan da ranar 28 ga wannan wata na Fabairu, ake sa ran wallafa rahoton kwararrun mai dubban shafuka da ya kunshi shawarwarin magance matsalar ta sauyin yanayi.
A wani labarin na daban a Wani binciken masana ya nuna cewar canjin yanayi ya sauya lokacin da ake samun ambaliyar ruwa a Turai, inda ake samun wasu koguna na cika da wuri, wasu kuma a makare, abinda ke matukar illa ga ayyukan noma da rayuwa baki daya a Yankin.
Farfesa Guenter Bloeschi na Jami’ar Fasaha ta Virginia da ya jagoranci binciken, ya ce a kasashe irin su Sweden da Findland da Yankin Baltic, a kan samu ambaliya wata guda kafin yadda aka saba gani a shekaru 1960 da 1970.
Shehun malamin ya ce a wancan lokacin a kan samu matsalar ce a watan Afrilu, amma a yau ana samu ne a watan Maris saboda narkewar dusar kankara da wuri.