An Kai Hari Da Makamai Masu Linzami A Yankin Arbil Na Kasar Iraqi.
Kamfanin dillancin labarun; Irna; na Iran ya nakalto wata majiya daga kasar Iraki tana cewa; An kai hare-haren ne dai akan wasu cibiyoyi guda biyu na kungiyar leken asirin HKI Musad dake birnin Arbil na yankin Kurdawa a Iraki.
Wata majiyar daga yankin na Kurdawa ta ambaci cewa A daren jiya an rika jin karar abubuwa suna fashewa a cikin birnin na Arbil.
Wata majiyar kuwa ta ambaci cewa; wani sansanin Amurka da yake a kusa da filin saukar jiragen sama a birnin na Arbil ya baci saboda saukar daya daga cikin makaman masu linzami da aka harba.
Kawo ya zuwa yanzu babu wani bangare da ya dauki alhakin kai harin.’
READ MORE : Putin ya ki ya gana da Ukrain a wata kasa idan ba Bilarusia ba.