Sakataren yace a bayyane take, wannan gidauniyar da aka kaddamar ba wai ta kunshi abinda za’a baiwa kasar ba ne, harma da bashin da kasar ke bin kasashen duniya.
Jawabin Antonio Guterres na zuwa ne kasa da wata guda bayan kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar ta Afghanistan, sakamakon rudanin da ya biyo bayan janyewar Amurka da kawayen ta.
Daga cikin Dala miliyan 606 da ake saran tarawa domin aikin jinkai a Afghanistan, akwai kudaden da za’a karkata wajen ciyar da jama’ar dake fama ad yunwa da kuma taimakawa marasa lafiya.
Sakataren yace Majalisar zata bada Dala miliyan 20 daga cikin asusun agajin gaggawan ta na Turai domin gudanar da aikin jinkai a Afghanistan, amma bukatar da ake da ita a kasar ta zarce abinda Majalisar ke da shi.