An Ji Karar Jiniyar Gargadi Na Tashi A Kiev Babban Birnin Kasar Ukrain A Yau Asabar.
An ji jiniyan gargadi suna tashi a birnin Kiev babbann birnan kasar Ukrai a safiyar yau Asabar a dai dai lokacinda majiyar fadar shugaban kasar Ukrain take cewa sojojin Rasha sun shirin farwa babban birnin kasar da wasu birana da dama a kasar da yaki.
Shugaban kasar ta Ukrain Volodymyr Zelensky ne ya bayyana haka a cikin wasu hotunan bidyo da ya aika a shafukan sadarwa na zumunta inda yake karfafa giwar mutanen kasar wajen nuna turkiyasaboda kare kasarsu daga abinda ya kira mamayar kasar Rasha.
READ MORE : An Kai Hari Da Makamai Masu Linzami A Yankin Arbil Na Kasar Iraqi.
A dayan bangaren kuma gwamnatin kasar Rasha ta kara jaddada bukatarta na cewa dole ne gwamnatin kasar Ukrain ta amince da cewa yankin Cremea ta zama kasar Rasha sannan yankunan Donbas kuma sun zama ‘yantattun kasashe daga kasar Ukrain, har’ila yau da kuma ta amince kan cewa ba zata shiga kungiyar NATO ba. Idan ta yi haka za’a tsaida bude wuta nan take.
A yau ne aka shiga kwanaki 17 da fara yaki a ukrain wanda ya zuwa yanzu ya tilisatawa miliyoyin mutanen kasar gudun hijira, sannan wasu daruruwa kuma suka rasa rayukansu.