An gurfanar da Ameerah a kotu bayan ta yi iƙirarin sace ta da mata 17.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar da matashiyar nan Ameerah Sufyan, wadda ta yi iƙirarin cewa wasu mutane sun sace ta tare da wasu mata masu ciki.
Matashiyar ta gurfana ne a kotun majistare da ke Abuja, babban birnin ƙasar da safiyar Laraba bisa rakiyar jami’an tsaro.
Daga cikin tuhume-tuhumen da suka yi mata, ‘yan sanda sun zargi Ameerah da tayar da hankali da yi wa rundunar ƙage saboda ta ce mutanen na sanye ne da kakin ‘yan sanda.
Sai dai bayan gabatar da tuhuma a kanta alƙalin kotun ya bayar da belinta saboda bincike ya nuna tana da lalurar ƙwaƙwalwa.
A ranar 14 ga watan Yuni ne Ameerah ta wallafa saƙo a shafinta na Twitter cewa wasu mutane sanye da kakin ‘yan sanda sun yi awon-gaba da su daga gidajensu a Abuja.
“Mu 17 ne, ciki har da masu ciki uku da yara biyu, amma ba su ga wayata ba,” kamar yadda ta wallafa a shafin nata.
A ‘yan watannin da suka gabata ma wata matashiya ta yi makamancin wannan iƙirari, inda har ta saka lambar wayan wanda ta ce shi ne ya je har gida don sace ta, kuma daga baya ta ƙaryata kanta.
‘Ameerah na da lalurar ƙwaƙwalwa’
Lauyar da take kare Ameerah ta faɗa wa kotu cewa gwajin da aka yi wa wadda take karewa ya nuna cewa matashiyar na da lalura a ƙwaƙwalwarta.
Bisa wannan dalili ne kuma suka nemi kotun ta ba da belinta, abin da mai shari’ar ya amince da shi.
Sai dai alƙalin ya sharɗanta wa Ameerah cewa wajibi ne ta dinga kai kanta ga rundunar ‘yan sanda duk wata na tsawon shekara ɗaya don tabbatar da tana shan maganin da likitoci suka rubuta mata.
‘Yarabawa ne da Fulani suka sace mu’
Da take wallafa saƙon na Twitter da misalin ƙarfe 1:40 na ranar 14 ga watan Yuni, Ameerah ta ce mutanen sun sace su ne daga ɓangarori daban-daban na birnin Abuja.
Ta ƙara da cewa ta tura tasawirar wuraren da ‘yan bindigar ke wucewa da su ga abokan hulɗarta ta dandalin WhatsApp don mutane su dinga ganin inda aka kai su.
Da take siffanta mutanen, ta ce: “Yarabawa ne huɗu da Fulani biyu. Sun rarraba mu. Mu bakwai ne a nan. Sun ce ɗaya motar za ta tafi Illorin, mu kuma tamu za ta nufi Ibadan ko Ikeja, kamar yadda suka faɗa.”
Wannan sanarwa da matashiyar ta wallafa ta jawo koke-koke da tir da Allah-wadai daga ma’abota Twitter a tsawon wannan rana, inda aka dinga sukar gwamnati da jami’an tsaron Najeriya kafin daga baya Ameerah ta ƙaryata kanta.
‘Ku yi min afuwa ƙarya nake yi’
Kwana uku da wallafa saƙon nata, rundunar ‘yan sanda ta ce ta gano inda take, sannan kuma da alama iƙirarin nata ba gaskiya ba ne.
Rundunar ta ƙara da cewa tana binciken matashiyar “kuma za mu sanar da mutane sakamakon bincike da zarar hali ya yi”.
Sai dai kuma, a ranar 20 ga Yunin Ameerah ta ƙaryata kanta, tana mai cewa “babu wanda ya sace ta”.
“Da gangan na fita daga gida, na kai kaina waɗannan wurare, na shiga daji kuma na galabaitar da kaina tsawon kwana huɗu haka kawai. Ina neman afuwa, ku yi mani addu’a saboda ina buƙatarta,” a cewar sabon saƙon da ta wallafa.
“Ina neman afuwar jama’a, da ‘yan sanda, abokaina, da dangina saboda ƙaryar da na yi musu. Babu wani abu mai kama da haka da ya faru, kawai tunanina ne maras kyawu.”