An Gudanar Da Zanga zangar Adawa Da Hana Sanya Hijabi A Makarantu A indiya.
Masu zanga zanga sun yi gangami a garin Jaipur domin nuna Adawa da hana sanya hijabi da aka yi a makarantu a garin Karnataka dake Kudancin kasar, bayan da aka sanar da hana mata musulmi sanya abin da zai rufe musu kansu a fadin makarantun kasar ta indiya
Zanga-zangar tana zuwa ne bayan da kwalejin chaksu ta hana wasu yan mata shiga aji saboda sun sanya hijabi day a rufe musu kansu, a makon jiya ma makarantu da dama a garin Karnataka sun hana mata musulmi shiga aji sabon da sun sanye da hijabi , inda suka bayyana cewa ministan Ilimi na kasar ne ya bada Izinin hakan ya jawo zanga zangar Iyayen yara da sauran dalibai.
Matakin harmata sanya hijabin a makarantu ya jefa fargaba tsakanin Alummar musulmi inda suka bayyana shi da cewa yana kara tsannata karkashin gwamnatin hindu mai rajin kishin kasa
Mafiyawancin musulmi a fadin Indiya na korafi
game da yadda suke fuskantar cutarwa da aikata laifuka daga maabiya Addinin
Hindu da kuma siyasar nuna wariya da gwamnatin kasar ke aiwatarwa