Wani alkalin birnin Paris na Faransa ya tuhumi tsohon shugaban kamfanin jirgin sama na Flash Air kan zargin sa da sakaci a aukuwar hatsarin jirgin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 148 a shekarar 2004 a tsibirin Sinai.
Daukacin fasinojin da ke cikin wannan jirgi ne suka rasa rayukansu da suka hada da Faransawa 134.
Yanzu haka, alkalin birnin Paris ya tuhumi Mohd. Nour, shugaban kamfanin jirgin a wancan lokaci, kuma shi ne mutun na farko da aka fara tuhuma bayan kwashe shekaru ana gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar hatsarin.
Bayan tsawon lokacin da ya dauka na kin amsa gayyatar alkalan Faransa, daga bisani Nour ya amince ya bayyana a gabansu domin amsa tambayoyi a cikin watan Satumba.
A cikin watan Disamban da ya gabata ne, alkalan Faransa suka sanar da Nour cewa, za a tuhume shi kan zargin kisa ba da gan-gan ba kamar yadda wata majiyar shari’a ta shaida wa jaridar Le Perisien.
Wani rahoton kwararru da ka fara fitar da shi a shekara ta 2008, ya nuna cewa, matukan jirgin ba su da ciakkken horo, sannan kuma sun galabaita matuka saaboda yawan aiki fiye da kima, abin da ya haddasa hatsarin a cewar rahoton.
A wani labarin na daban Tun ranar daya ga watan da muke ciki na Janairu ne shugaba Emanuel Macron na Faransa ya fara jan ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar turai, inda kungiyar za ta maida hankali kan batutuwan huldar diflomasiya tsakaninta da nahiyar Afrika, a zaman taron da za ta gudanar na ranakun 17 da 18 ga watan fabrairu 2022.
Za a iya cewa dai kafin gudanar da zaman taron shugaba Emmanuel Macron na da babban abokin kawance ga zaman taron cewa da, shugaban kasar Senegal Macky Sall da zai karbi jagorancin kungiyar tarayyar Afrika a farkon wannan shekara ta 2022.
Shuwagabannin kasashen 2 dai tun a ranar 20 ga watan December da ya gabata suka tattauna batun samun goyon bayan junansu a wajen taron.
Bayan haka kuma rahoton zaman taron watan septembre da ya gabata ya dai dai kanun kasshen 27 na turai da 55 na kasshen kungiyar tarayyar Afrika kan batutuwan da dama da zaman taron nasu zai tabo da suke da sabaani a kai.
Haka kuma Shugaban Senegal ya bayyana cewa, wa’adin shugabancinsa na kungiyar tarayyar Afrika zai maida hankali ne kan batun martaba adalci wajen cinikin ma’adanan karkashin kasa da kuma samar da sauyi game da yadda ake gudanar da jagorancin duniya.