An Fara Tattaunawar Neman Ceto Yarjejeniyar Nukiliyar Iran A Doha.
Karamin ministan harkokin wajen Iran, kana kuma mai jagorantar tawagar kasar a tattaunawar neman farfado dayarjejeniyar nukiliyar Iran, Ali Bagheri Kani, ya isa birnin Doha na kasar Qatar a wannan Talata inda yake halarci sabon zagayen tattaunawar neman ceto yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a 2015.
Mista Kani, ya gana da mukadashin babban jami’in kula da manufofin ketare na kungiyar tarayyar Enrike Mora a birnin na Doha.
Kafin nan dama wakilin musamman na Amurka kan Iran, Robert Malley, shi ma ya isa birnin Doha a ranar Litini game da tattaunwar wace ke gudana amma ba kai tsaye ba tsakanin Amurka da Iran.
Bayanai sun ce tattaunawar dai za ta maida hankali ne kan batutuwan da Amurka da Iran suke da sabani akansu, wadanda suka hana cimma matsaya kan yarjejeniyar.
READ MORE : Sabon Fira Ministan Somaliya Ya Karbi Ragamar Jagorancin Kasar A Hukumance.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Iran da kungiyar tarayyar turai suka amince da komawa bakin tattaunawar da aka faro a Vienna da nufin dagewa Iran jerin takunkuman da aka kakaba mata.
READ MOER : Bulgariya Ta Kori Jami’an Diflomasiyyar Rasha Guda 70 Daga Kasarta.