An fara baiwa wasu fitattaun mutane da suka taka rawa a fannoni da dama lambar yabo ta Nobel, inda wasu kwararru a fannin da ya shafi lafiya da suka hada da David Julius da Aderm ‘yan asalin kasar Amurka suka lashe kyautar.
Bisa al’ada dai, akan zabi wasu fitattaun mutane a duniya da suka taka rawa a fannoni da dama don ba su wannan lambar yabo ta Nobel mai matukar muhimmanci.
A bana, an fara bayar da kyautar ce daga fannin kimiyya da lafiya, inda za a ci gaba da bayar da ita a na fannin har-hada magunguna a gobe Talata, sai fannin har-hada sinadarai da za a bada a ranar Laraba.
Za a bayar da kyautar a sashen adabin Turanci wato Literature a ranar Alhamis, sai na zaman lafiya wadda kusan ita ta fi kowacce muhimmanci da za a bayar da ita a ranar Litinin na makon gobe.
Kamar kowanne fanni dai, cutar Corona ta shafi tsarin bayar da kyautar yabon da ake yi kowacce shekara, sai dai duk da an yi a bana, amma dai an kula sossai wajen tara jama’a da kuma tabbatar da biyayya ga dokokin kare yaduwar cutar.
A wani labarin na daban adadin mutane da annobar korona ta kashe a kasar Amurka ya zarce dubu mutane dunu 700 tun bayan barkewar cutar zuwa ranar Juma’a.
Wannan adadi da Jami’ar Johns Hopkins na Amurkan ta fitar shine mafi yawa da aka taba gani a duniya, inda ya yi daidai da yawan jama’ar babban birnin kasar Washington.
Wannan na zuwa ne yayin da adadin wadanda cutar ke kashewa kulla yaumin ke kaiwa sama da dubu 1, a kasar da kashi 55.7 da al’ummarta suka karbi allurar rigakafin cutar.
Korona na ƙara yaɗuwa a Amurka musamman sabon nau’in Delta, inda lamarin ya fi kamari a jihohin kudancin kasar.
Amurkan dai na fama da matsalolin da ake hasashen na iya durkusar da ita.