Sama da rakuma 40 aka cire daga cikin wadanda za su shiga gasar sarauniyar kyau a kasar Saudiyya, saboda an yi musu allurar kara girman mazaunai da kara kyau.
Gasar wani bangare ne na bikin kalankuwar sarki Abdulaziz, kuma duk wadda ta yi nasarar lashewa za ta tafi da zunzurutun kudi har dala miliyan 66.
Cikin abubuwan da ake dubawa, akwai girman leben rakuma, da babban hanci, da kuma mulmulallen tozo.
Alkalai sun yi amfani da fasahar zamani domin gano wadanda ba su bi ka’ida ba a gasar, da dora su a kan sikeli kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SPA ya rawaito.
Dukkan wadanda za su shiga gasar ana jere su ne a wani katon dakin taro, inda kwararru za su bincike su tsaf domin duba cancanta ko akasin haka.
Ana duba kawunansu, da wuya, da kofato, ta hanyar yi musu hoto ta amfani da sabbin injina masu ingancin fasahar zamani, za kuma a dauki samfurin kwayoyin halittarsu domin gwaji.
An cire rakuma 27 daga cikin tawagar Majaheim, saboda an mikar da jikinsu, yayin da 16 kuma aka yi musu allurai, in ji SPA.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
An ambato masu shirya gasar na kungiyar masu rakuma, na cewa sun dauki alkawarin za su cire duk rakuman da aka yi wa kwaskwarimar da ta saba wa ka’idojinsu, za kuma su sanya tara mai tsanani ga wadanda suk saba wa doka.
Sun yi bayanin yadda ake yi yiwa rakuman allurar kara kyau da girman lebe, da hancinsu, da muka-muki, da wani bangaren na kan su, da allurar kara sheki, da girman hanci, da kuzari da wanda zai sanya su girman jiki.
Ana amfani da kyauro a jikin dabbobi domin sanya wasu sassan jikinsu girma, ta hanyar hana jini gudana a wajen.
Jason Baker, babban mataimakin shugaban kungiyar kare hakkin dabbobi Peta Asia, dya bayyana gasar sarauniyar kyan dabbobin da abu na “rashin imani”.
“Duk wata dabba da aka yi wa kwaskwarima, kama daga huda musu kunne da sanya musu dankunne mai nauyi, da allurar kara kyau, kawai domin a nunawa mutane wannan tsabar rashin imani ne da tausayi, kuma abubuwa ne da idan dan adam ya yi ya ke sanya shi muni,” in ji shi.
Mista Baker ya kara da cewa ana bukatar daukar mataki wajen jaddada muhimmancin kula da jin dadi da walwalar dabbobi a yankin Gabas ta Tsakiya da Asiya, ya kuma yi kira ga hukumomin Saudiyya su haramta yin irin wannan gasa da ke janyo cin zarafin dabbobi.
Akalla masu rakuma 33,000, daga kasashen Amurka, da Rasha da Faransa da Gabas ta Tsakiya ne suka shiga gasar ta Sarki Abdulazizi, wadda ita ce mafi girma a duniya da ake daukar kwanaki 40 ta na gudana.
Har wa yau, ‘yan yawon bude ido 100,000 ake sa ran za su halarci dandalin da ake yi gasar mai girman sukwaya mita 33 da ke arewa maso gabashin babban birnin Saudiyya wato, Riyadh.