An Bukaci Gwamnatin Lebanon Ta Gaggauta Kammala Yerjeniyar Sayen Makamashi Daga Iran.
Shugaban jam’iyyar ‘Tauhid Al-Arabi” na kasar Lebanon ya bukaci gwamnatin firai minister na rikon kwarya Najib Mikata ta gaggauta kammala yerjiniyar sayen makamashi daga kasar Iran.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Wi’am Wahhab shugaban jam’iyyar Attauhidul Arabi yana fadar haka a shafinsa na twitter, ya kuma kara da cewa yakama firai minister Najib Mikati ya nuna jarunta, ya tura ministan makamashin kasar zuwa Tehran don kammala yarjejeniyar sayan makamashi daga kasar ta Iran.
Kafin haka dai shugaban kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon ya fadawa gwamnatin kasar kan cewa a shirye yake ya shigo da makamashi daga kasar Iran amma da sharadin gwamnatin kasar ta amince da hakan.
READ MORE : Sojojin Najeriya Sun Sake Kama Babban Dan Kungiyar ISWAP Wanda Ya Tsere Daga Kurkukun Kuje.
Kasar Lebanon dai tana fama da karancin makamashi mai tsanani a cikin yan watannin da suka gabata, wanda ya kai ga hatta asbitoci basa da wuta, hakama wasu gidajen gasa buredi sun rufe saboda rashin wuta.
READ MORE : Iran; Cibiyar Sararin Samaniya Ta Karbi Sakonni Na Farko Daga Tauraron Dan’adam Mai Suna “Khayyam”.