An Bude Taron Tattaunawa Na Kasa A Birnin N’Djamena Na Kasar Chadi.
Ajiya Asabar ce aka bude babban taron Tattaunawa na kasa a kasar Chadi ind a shugaban mulkin soji na kasar Janaral Mahamat Idriss Debay ya bayyana taron a matsayin lokacin mafi muhimmanci ga Alummar kasar,
An ware makwanni 3 domin bada dama ga wakilai sama da 1400 daga bangaren gwamnati da kungiyoyin farar hula da jam’iyun adawa da sauran kungiyoin yan tawaye a kasar , tattaunawa kan zaman lafiya da kafa sabon kundin tsarin mulki a kasa ta biyar a girma a nahiayr Afrika
Sai abu mai muhimmaci game da taron shi ne zai bude hanyar gudanar zabuka a kasar kafin karshen watan oktoba da mai kamawa , Mahamat idris deby wanda yah au karagar mulkin kasar bayan mutuwar mahaifinsa a watan Aprilun shekara ta 2021 ya sha alwashin shriya zabukan na demukuradiya akarshen gwamnatin rikon kwaryar kasar bayan watanni 18.
READ MORE : Fursunonin Falasdinawa Za su Fara Gudanar da Yajin Cin Abinci Na Gama gari A Gidajen Kurkukun Isra’ila.
Wannan taron yana zuwa ne bayan rattaba hannun kan yarjejeniyar sulhu tsakanin kungiyoyin adawa sama da 40 a kasar da kuma gwamnatin mulkin soji ta kasar a ranar 8 ga watan Agustan da muke ciki a birnin Doha.