An Ayyana Dokar Hana Fita Ta Sa’o’I 36 A Birnin Kiev Na Ukraine.
An ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’I 36 a Kiev babban birnin kasra Ukraine, a daidai lokacin da bayanai ke cewa ana kai hare hare a wasu unguwanni na birnin.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka shiga kwana na 21 na rikicin Rasha da Ukraine din.
A wani lokaci yau ake sa ran bangarorin zasu sake komawa bakin tattaunawa a karo na biyar.
Hukumar kula da kaurar jama’a ta MDD, ta bayyana cewa sama da mutum miliyan uku ne suka tsarewa rikicin Ukraine.
READ MORE : Koriya Ta Arewa Ta Harba Wani Makami Da Bai Yi Nasara Ba.
Haka zalika Kimanin mutane 20,000 ne suka samu fida daga birnin Marioupol a ranar Talata ta hanyoyin da akayi tanadi domin ayyukan jin kai.