Tun a watan Oktoban bara da Isra’ila ta kaddamar da farmaki a Gaza, ta hanyar amfani da makaman da akasarinsu daga Amurka take samu, Amurkawa da dama sun fara tunanin yiwuwar daina daukar nauyin kisan gilla da kudinsu.
Amurka tana ba Isra’aila agajin soji na sama da Dala biliyan uku duk shekara, sannan ta kara yawan agajin tun daga Oktoban bara da aka fara yakin.
Sannan daga Yakin Duniya na biyu, Amurka ta ba Isra’ila taimakon soji sama da wata kasa a duniya, inda adadin kudin da Amurka ta kashe wajen tallafin sojin ya kai Dala biliyan 317.
Bayan cire tallafin Social Security da na Medicare, wadanda dukansu wasu kudade ne da ake warewa kuma ake kashewa daban daga kudaden haraji, Kungiyar War Resistance League ta ce ayyukan soji ne ke lakume kusan kashi 45 na kasafin kudin kasar. A Kasafin Kudin Shugaban Kasa Biden na shekarar 2025, wannan kason na nufin Dala triliyan 2.25.
Dukkan kudin nan ana samunsu ne daga kudin harajin mutanen Amurka, ko suna so, ko ba sa so.
Amma yanzu an fara samun masu nuna turjiya.
Kin biyan haraji
Kungiyar Kin biyan haraji wato The National War Tax Resistance Coordinating Committee (NWTRCC) ya samo asali a shekarar 1982, inda wasu kungiyoyi masu ra’ayi iri daya suka hadu domin adawa da harajin soja.
A takaice, abin da suke so shi ne a daina biya dukkan haraji ko wasu daga cikin harajin Gwamnatin Tarayya.
Sanin hakikanin adadin wadanda ba sa son biyan harajin da kamar wuya, amma dai za su iya haura mutum 10,000. Kafin farmakin Gaza da Isra’ila ta yi, shafin intanet na NWTRCC na samun masu ziyarar musamman guda 40,000 duk shekara, amma yanzu muna samun kusan 20,000 duk wata.
A farko-farkon watan Nuwamba, da mutane suka fara ganewa tare da fahimtar da’awar NWTRCC, sai da shafinmu ya tsaya cak. An sake samun hakan sau biyu a karshe-karshen shekarar 2023, har sai da ala dole muka bunkasa shafin.
Mutane suna ziyartar shafinmu ne domin su fahimci yadda za su rage wasu daga cikin harajin da suke ba gwmanati. Sannan suna so su fahimci girman laifin da zai hau kansu idan suka ki biyan harajin.
A Amurka, laifi ne mutum ya ki biyan haraji. Amma a cikin gomman shekarun da suka gabata, kasar ba ta gurfanar da mutane da yawa ba bisa laifin kin biyan haraji.
Yakin ya-ki-ya-ki-cinyewa
Bayan halin da ake ciki a Gaza, Amurka na cigaba da “yaki da ta’addanci” da ta dade tana yi ta hanyar amfani da jirage marasa matuka a kasashe irin su Afghanistan da Syria da Yemen. Haka kuma Amurka tana da sojoji a sama da sansanonin soji guda 800 a fadin duniya.
Kin biyan haraji wata hanya ce ta hawa teburin na ki.
A wajen wasunmu da muka ki shiga aikin soja, muna ganin me zai sa kuma mu dauki nauyin yaki?
Wannan tambayar ce ta sa Amurkawa da dama suka daina biyan haraji a lokacin yakin Vietnan da wasu yakokin.
A shekarun 1990s ne na fara tunanin daina biyan haraji bayan na ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka na wancan lokacin, Madeleine Albright na bayyanawa a wata tattaunawa cewa dubban kananan yaran da suka mutu a Iraqi saboda yunwa “sun cancanci” mutuwa.
Tun wancan lokacin na daina biyan harajin na radin kaina. A game da harajin, Kungiyar NWTRCC tana shirya tarukan wayar da kan mutane duk mako na yadda za su fahimci matsalolin da suke tattare da kin biyan haraji.
Daga cikin masu daukar nauyin tarukan har da Kungiyar Lauyoyi da Kungiyar Ma’aikatan Lafiyar Falasdina na San Francisco.
Yawancin masu shiga fafutikar matasa ne ’yan kasa da shekara 30, sannan akwai mutane daga kowane bangare na duniya.
Yawanci ta Instagram ne suke samun bayani game da tafiyar, inda shafinmu yake ta samun karbuwa.
DUBA NAN: Jami’ai Sun Kama Masu Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Amurka
Kafin farmakin Gaza, masu bibiyan shafinmu ba su wuce 500 ba, amma yanzu mun kusa 20,000.