Amurka Zata Rage Takunkuman Da Ta Dorawa Venezuela Da Sharadin Ta Saida Mata Man Fetur.
Tawagar kasar Amurka wacce ta kai ziyara irinta na farko zuwa kasar Venezuela tun shekara ta 2019, ta amince zata ragewa kasar Venezuela takunkuman saida man fetur da ta dora mata, amma da sharadin zata ware wani kaso daga cikinsa don sayarwa kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa har ila yau kasashen biyu sun tattauna bakin daukewa kamfanin man fetur na kasar Venezuela da babban bankin kasar takunkuman sadarwa tsakanin bankuna don su sake komawa cikin kasuwannin duniya.
Amurka dai tana neman inda zata sami man fetur bayan da ta dorawa kasar Rash takunkuman tattalin arziki, daga ciki har da sayan man kasar, saboda mamayar da tayiwa kasar Ukrain.