Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da sabon shirin gwamnatinsa na mikawa kasar Ukraine tallafin karin makaman da darajarsu ta kai dala biliyan daya.
Matakin na Amurka ya biyo bayan rokon karin tallafin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy yayi a baya bayan nan domin karfafawa dakarunsa gwiwa dake fafatawa da na Rasha.
Sai dai wasu daga cikin masu sharhi kan lamurran dake wakana, sun yi gargadin cewa tarin makaman da Amurka da sauran kasashen Turai ke baiwa Ukraine a matsayin tallafin yakar Rasha, ka iya zama kalubale babba ga tsaro a sassan Turai nan gaba, la’akari da rahotannin yiwuwar fantsamar da makaman ke yi zuwa wuraren da ba a yi nufin su kai ba.
Cikin makwannin baya bayan nan dakarun Rasha suka bayyana cewa suna dab da kammala kwace iko da Severodonetsk, wani muhimmin birni mai arzikin masana’antu a yankin Lugansk da sojojin Ukraine suke ta kokarin karewa.
Samun nasarar kame birnin Severodonetsk ya zama babban burin Rasha, la’akari da cewar shi ne zai zama hanyar zuwa wani babban birnin mai suna Sloviansk dake yankin Kramatorsk.
A wani labarin na daban kasar Rasha ta ce ta haramtawa wasu Amurkawa 963 shiga kasarta ciki har da shugaban Amurka Joe Biden da sakataren harkokin wajensa Antony Blinken da kuma shugaban CIA William Burns.
Haramcin tafiye-tafiye na da dan tasiri, a wani bangare dake tabbatar da tsamin dangantakar Rasha da Amurka da kawayenta tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.
Wannan na zuwa ne yayin da Katafaren kamfanin makamashi na kasar Rasha Gazprom ya sanar da dakatar shigar da iskar gas zuwa makwabciyar kasar Finland saboda kin amincewa da biyan ta da kudin kasar ruble.
Moscow dai ta bukaci abokan cinikinta daga “kasashe da basa ga maciji – ciki harda kasashe membobin EU – da su rika biyan kudin cinikin iskar gas da Rubels dinta, domin kaucewa takunkumin karya tattalin arzikin da kasashen Yamma suka kakaba mata bayan mamayar Ukraine.