Amurka za ta horar da sojojin Ukraine kan amfani da makamin kariya daga hare-hare samfurin Patriot
Gwamnatin Amurka ta sanar cewa kimanin sojojin Ukraine za su isa kasar a farkon makon gobe domin a fara horar da su kan sarrafa makamai samfurin Patriot missile system.
Wadanda ke iya samar da kariya daga hare-haren da Rasha ke kai wa Ukraine da makamai masu linzami.
Gwamnatin ta ce za a ba sojojin horo na musamman cikin takaitaccen lokaci, lamarin da ke nufin za a iya girke makaman gabanin lokacin da Amurkar ta sanar a baya.
Yayin wata ziyara da ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta kai birnin Kharkhiv na kasar Ukraine, an yi wasu kiraye-kiraye ga Jamus din ta ba Ukraine wasu tankokin yakinta samfurin Leopard.
Cikin wata hira da yayi da BBC, wani mai ba ministan tsaron Ukraine shawara Yuriy Sak, ya bayyana dalilan da suka sa kasarsa ke bukatar tankokin yaki daga kawayenta na yammacin Turai:
“Idan ana batun mayar da martanin yaki, tankokin yaki na da muhimmanci matuka, kuma dakarun Ukraine a wanna lokacin na da jajircewar da ake bukata domin yantar da kasarmu, amma fa sai da taimakon tankokin yaki daga kasashen yammacin Turai.”
Ya kara da cewa, “Irin samfurin tanki na Abrams da Leopard Two sune wadanda za su bamu damar kutsawa cikin hanzari zuwa yankunan da abokan gaba ke rike da su. Mun san cewa kawayenmu na yamma na da dubban tankokin yakin, amma muna bukatar ‘yan daruruwan tankokin ne kawai.”
Makaman na Patriot na cikin rukunin makaman samar da kariya daga hare-hare daga sama mafi nagarta da bayar da kariya daga makamai masu linzami a fadin duniya.
A martanin da Rasha ta mayar, ta ce da zarar makaman sun isa Ukraine, za ta mayar da hankalinta ne wajen lalata su baki daya.