Amurka za ta ƙara yawan makaman da take bai wa Ukraine.
Jami’an Amurka sun ce gwamnatin Shugaba Joe Biden na kokarin ƙara yawan makaman da take bai wa Ukraine.
Amurka ta bai wa Ukraine taimakon makamai da agajin da ya kai na dala biliyan ɗaya da miliyan bakwai tun bayan soma yakinta da Rasha.
Daga cikiin makaman da Amurka ta bai wa IUkraine akwai nakiyoyin da ke lalata tankokin yaki da masu kakabe makamai masu Linzami, wadanda ke taimakawa wajen kare birnin Kyiv.
Shugaba Zelensky na Ukraine ya sake kara rokon karin manyan makamai da jiragen yaki da makaman atilare domin fuskantar Rasha da ke kokarin mamaye gabashin kasar baki daya.
READ MORE : Ya kamata Buhari ya sauka daga mulki saboda ba zai iya magance matsalar tsaro ba – Ƙungiyar Dattawan Arewa.
Ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon, za ta tattauna da manyan kamfanonin kera makamai a yau Laraba domin nazari kan karin taimakon da za a bai wa Ukraine ɗin.
READ MORE : Iran Ta yi Tir Da Harin Makami Mai Linzamai Da Isra’ila Ta Kai A Kasar Siriya.