Amurka ; Yan Sanda Na Farautar Mutumin Da Ya Bude Wuta Kan Jama’a A New York.
Rundunar ’yan sandan birnin New York na Amurka, ta ce tana ci gaba da farautar mutumin da ya bude wuta a tashar jirgin karkashin kasa ta Brooklin inda ya raunata mutum kimanin 20 a ranar Talata.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne, lokacin da wani jirgin kasa ke tsayawa a tashar dake kusa da Sunset Park, wani mutum da ya rufe fuskarsa, sanye da rigar ma’aikatan gine-gine, ya bude wuta kan mutanen dake cikin jirgin, da ma wadanda suke waje kusa da jirgin.
’Yan sanda sun ce za su kara tsananta bincike game da musabbabin aukuwar harin.
Da take karin haske kan hakan, mataimakiyar kwamishinan ’yan sandan birnin Laura Kavanagh, ta shaidawa manema labarai cewa, 5 daga cikin wadanda aka harba na cikin halin mutu kokwai rai kokwai.
READ MORE : Ministan Tsaron Kamaru Ya Koka Kan Yawan Shingayen Binciken Ababen Hawa.
A daya hannun kuma, an yiwa shugaban Amurka Joe Biden, cikakken bayani game da aukuwar wannan lamari, kamar dai yadda wata majiyar fadar White House ta tabbatar.
READ MORE : Sojin Isra’ila Sun Sake Kashe Wani Bafalasdine.
READ MORE : Oxfam : Mutum Miliyan 250 Na Fuskantar Matsanancin Talauci A Duniya.