Gwamnatin Birtaniya ta ce tana da tabbas wasu gungun yan ta’adda na shirin kai hare-hare a Amurka.
Hakan yasa gwamnatin Birtaniya, cikin sanarwar shawarwari ga matafiya, a ranar Juma’a 4 ga watan Nuwamba ta gargadi yan kasarta da ke Amurka su yi taka tsantsan kuma su rika sauroron kafafen watsa labarai.
Gwamnatin ta bayyana cewa wadanda za su kai harin mutane ne wadanda suka yi imani da akidar yan ta’adda.
Kasar Birtaniya cikin sanarwar bada shawarwari ga masu tafiye-tafiye ga yan kasarta, a ranar Juma’a ta yi gargadin cewa yan ta’adda na shirin kai hari Amurka.
Ta shawarci yan kasarta da ke Amurka su yi taka tsantsan kuma su guji zuwa wuraren taruwan mutane, The Nation ta rahoto.
Birtaniya Ta Gargadi Amurka Cewa Yan Ta’adda Na Shirin Kawo Mata Hari.
Wuraren da ake zargin yan ta’addan za su kai harin a Amurka, in ji Birtaniya.
A cewar Birtaniya, akwai yiwuwar yan ta’addan za su kai hari inda baki ke taruwa ko wuraren taruwar mutane da tashohin zirga-zirga.
A baya-bayan nan, Legit.ng ta rahoto cewa Amurka da Birtaniya sun gargadi yan kasarsu cewa akwai yiwuwar yan ta’adda za su kawo hari Abuja.
Vanguard ta rahoto cewa hukumar yan sandan FBI ta gargadi Amurkawa a New Jersey cewa yan ta’addan na shirin kai hari a wuraren ibadu.
FBI ta ce ta samu sahihin bayanin sirri game da barazanar kai hari a wuraren bauta a New Jersey tana mai kira su dauki matakin kare iyalansu.
Sanarwar ta ce: “Akwai yiwuwar yan ta’adda za su kawo hari a Amurka.
Ana iya kai harin a ko, ciki har da wuraren da baki ke zuwa, wurin taruwa mutane da cibiyoyin sufuri. Ku rika duba kafafen watsa labarai kuma ku zama masu taka tsantsan.
“Babban barazanar ta fito ne daga daidaikun mutane wadanda watakila akidar ta’addanci ta sanya su kai hare-hare da ake kira ‘Harin kai kadai’ da ake kaiwa kan al’umma ko wurare.
Hare-hare na iya faruwa ba tare da an lura ba.”
Dangane da gargadin, gwamnatin Birtaniya ta ce akwai yiwuwar Amurka za ta tura jami’an tsaro zuwa wuraren taruwar mutane don dakile yiwuwar kai harin, ta kara da cewa hukumar tsaro ta Homeland ta fitar da gargadi mai inganci game da yiwuwar harin.
Source:legithausang