Amurka ta yi watsi da tayin Rasha na tattaunawa da Ukraine wanda ta kira da mai cike da shiririta yayinda ta bukaci Moscow ta gaggauta janye dakarunta daga Kyiv.
Kiran na Amurka na zuwa a dai dai lokacin da kasar tare da Tarayyar Turai ke lafta wani sabon takunkumi kan shugaba Vladimir Putin da ministan harkokin wajensa Sergei Lavrov.
Shugabancin Ukraine na ci gaba da neman taimakon kasashen yammaci da Amurka don dakile barazanar Rasha da ta afkawa sassan kasar sa’o’i 24 da suka gabata, sai dai shugaba Joe Biden ya nanata cewa Amurka ba za ta tura dakaru Ukraine a yanzu ba.
Sai dai Kungiyar tsaro ta NATO ta sanar ad shirin girke dakaru a kasashen mambobinta daga gabashi don baiwa al’ummarta kariya daga Rasha.
A bangare guda cikin wani gajeren faifan bidiyo da shugaba Volodymyr Zelensky ya saki da yammacin yau ya ce bazai bar kasar ko kuma ajje mulki kamar yadda Putin ya bukata ba.
A cewar Zelensky za su zauna a Ukraine ba gudu ba ja da baya har sai sun yi nasara kan Rasha.
Zuwa yanzu mutane fiye da dubu 50 suka tsere daga Ukraine yayinda wasu 137.
A wani labarin na daban tuni Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da kaddamar da ayyukan soji a kan kasar Ukraine bayan share tsawon makwanni ana zaman tankiya da kuma gazawar matakai na diflomasiyya tsakanin Rasha da kasashen Yammacin Duniya.
Putin, ya ce ya dauki wannan mataki ne domin kauce wa faruwar kisan kiyashin da mahukuntan birnin Kiev suka tsara aiwatarwa a yankin tare da kawo karshen take-take irin na tsokana da kasashe mambobi a kungiyar NATO ke yi wa Rasha.
Ministan tsaron kasar ta Ukraine Dmytro Kouleba ya ce Rasha ta tsara gagarumin shirin mamaye kasar, kuma tun a sanyin safiyar yau ta fara kai hare-hare da kuma jin karar fashewar abubuwa a wasu biranen kasar ciki har da birnin Kiev. Tuni dai Ukraine ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga jiragen da ke jigilar fasinja,
Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci tsagaita wuta a cikin gaggauwa, sai kuma shugaba Joe Biden na Amurka wanda ya yi tir da wannan farmaki na Rasha yayin da kungiyar tsaro ta NATO ke shirin gudanar da taron gaggawa kan lamarin a yau alhamis.