Amurka ta yi amai ta lashe a kan shugaban Rasha.
Fadar gwamnatin Amurka, White House, ta ce kalaman da Shugaban kasar Joe Biden ya yi na cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ba zai ci gaba da mulki ba, ba yana nufin kawo karshen gwamnatinsa ba ne.
A lokacin da yake gabatar da jawabi kai tsaye ba daga wata takarda ba da aka rubuta jawabin, a karshen ziyararsa a Poland, Shugaba Biden ya ambata cewa, Putin ya dukufa ne da aikata tashin hankali tun daga farko, saboda haka, ”ba za a bar shi ya ci gaba da mulki ba.”
Daga baya ne wani jami’in fadar gwamnatin Amurkar ya fassara kalaman da cewa Shugaban ba yana nufin kawar da gwamnatin Putin ba ne, ya ce, ”abin da yake nufi shi ne ba za a bar Shugaba Putin ya ci gaba da nuna iko a kan makwabtansa ko yankin ba.”
A zafafan kalaman da ya gabatar a jawabin na birnin Warsaw, Mista Biden, ya zargi Rasha da yunkurin yi wa dumukuradiyya kanshin-mutuwa a Ukraine da kuma son yin haka a wani wurin ma.
Shugaba Biden ya ce tirjiyar da Ukraine ta yi a kan yunkurin mamayen na Rasha wata gwagwarmaya ce ta tabbatar da ‘yanci, yana mai gargadin ci gaba da fadan har wani tsawon lokaci.
A martaninta fadar gwmnatin Rasha, Kremlin ta ce al’ummar Rasha su ke da ikon sauya gwamnatinsu ta zabe.
Tun da farko shugaban na Amurka ya bayyana takwaran nasa na Rasha a matsayin mai zubar da jini, bayan ya gana da wasu matasa ‘yan gudun hijira na Ukraine, wadanda suka tsere wa yakin zuwa Poland, kuma a yanzu suke tallafawa a aikin jinkai na ‘yan gudun hijira.
Shugaban ya ce kowanne daga cikin ‘yan gudun hijirar matasa ya bukace shi da ya yi wa ko dai mahaifi ko kuma wani dan uwansa addu’ar tsira lafiya daga yakin a can kasarsu, Ukraine.
Kafin sannan shugaban ya tattauna da takwaransa na Poland, Andrzej Duda.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai daga baya, Mista Duda, ya ce ya bukaci duba yuwuwar hanzarta kai wa kasarsa jiragen saman a yaki da igwa-igwa da makamai masu linzami, daga Amurka, domin taimaka wa karfafa tsaro a Poland.
Shi ma da yake magana da BBC daga baya kakakin ma’aikatar harkokin wajen Poland, Lukasz Jasina , ya yaba wa Mista Biden da kuma jawabin da ya gabatar.
Ya ce, ”Shugaban kasa mafi karfi a duniya ya zo Warsaw kuma ya yi jawabi a fili karara a kan mamayen Rasha, da matakin Mista Putin a kan halin da ake ciki a Ukraine.”
”Ya fayyace karara wanda yake da alhkin yakin da ake yi a Ukraine. Kuma ya ce wanda ke da wannan alhaki a kansa shi ne Mista Putin.
Sannan ya gaya wa ‘yan Rasha cewa har kullum akwai lokacin da za a sauya dan kama-karya. Yanayi ne mai tsanani da tayar da hankali.” in ji kakakin.
Mista Jasina ya ce za a sake karbar Rasha ne a cikin gamayyar kasashen duniya, idan ta samu sabon shugabanci kawai:
Ya ce, ”Ba za a sake karbar Putin ba a cikin gamayyarmu ta kasashen duniya, ba za a sake saurarensa ba, ba abokin tafiya ba ne da za mu yarda da shi ba.”
”Idan ba shi ne kadai za a iya dakatar da yakin nan, za a iya dakatar da kutsen da Rasha ta yi a Ukraine, sannan kuma Rasha za ta iya zama wata kawa mai amfani a wurinmu gaba daya.” in ji shi.
Ya kuma bayar da shawarar yin kokari daga cikin fadar gwamnatin Rashar na kawar da Shugaba Putin.