Amurka Ta Tsawaita Takunkuman Tattalin Arziki A Kan Zimbabwe.
Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa ta tsawaita takunkuman tattalin arzikin da ta kakabawa kasar Zimbabwe tun shekara ta 2003.
Jaridar The Nation ta kasar Kenya ta nakalto shugaban kasar Amurka Joe Biden yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa shugaban kasar Zimbabwe Emerson Nnagwagwa bai aikata sauyae-sauyen da ya yi al kawari zai aikata ba bayan ya karbi mulki daga hannun tsohon shugaban kasar marigayi Robert Mugabe. Banda haka shugaban ya ce haryanzun ana takurawa yan adawa da kuma ‘yan jaridu a kasar ta Zimbabwe.