Kwamandan sojin Iran Abdrrahman Mosavi ya bayyana cewa gwamnatin amurka ta shiga rudani da halin rikicewa sakamakon yadda sojin ruwan Jamhuriyar musulunci ta Iran suka iya aiwatar da muhimmin aikin su a tekun atlanta kuma suka dawo gida cikin nasara ba tare da wata kasa ta iya tankiya dasu ba tsahon wannan muhimmin aiki, kuma sojin ruwan na jamhuriyar musulunci ta Iran basu nemi taimakon kowacce kasa ayayin gudanar da wannan muhimmin aiki wanda ya kara fito da karfin sojin Iran din a fili hakan kuma yana zaman jan kunne ga amurka da yaran ta wadanda ke ganin zasu iya ma Iran din katantsaye a sabgogin da suka shafe ta.
A ranar lahadi ne dai kwamandan sojin na Iran, Abdurrahman mosavi ya bayyana hakan yayin da yake tarbar bataliyar sojin ruwa ta 75 a birnin Tehran inda ya bayyana cewa wannan nasarar aikin da sojojin jamhuriyar musulunci ta Iran din suka samu ya sanya makiya dole sun duba yiwuwa canja salo kuma ya jefa tsoro a zukatan makiyan jamhuriyar ta musulunci.
Kwamandan na sojin Iran din ya bayyana cewa ta bayyana a fili cewa babu wata kasa da zata iya bama Iran din matsala a duk abinda ta sanya a gaba, ko da amurka ce kuwa, domin wannan aiki da sojin Iran din suka aiwatar ya danagana dasu har kusa da iyakokin manyan kasashen da suke ganin sun fi kowa karfin soji amma basu iya tankiya da sojin na jamhuriyar musulunci ta Iran ba.
Kwamandan ya tabbatar da cewa takunkuman tattalin arzikin da amurka ta kakabawa Iran sun bayyana a matsayin wata babbar dama ga Iran din na fadada tunani domin cimma manya manyan hadafi a cikin kankanin lokaci kuma alokaci guda ta nuna cewa takunkuman tattalin arzikin basu da wani tasiri a kan jamhuriyar musulunci ta IRAN.
Wannan dai itace tafiya mafi nisa da sojin Iran din sukayi a teku, wanda hadafin tafiyar shine nuna isa gami da karfin sojin Iran ga duniya.
Tafiya kilomita dubu arba’in da biyar kuma an bi ta kasashe 55 kuma ta cikin nahiyoyi 3 cikin nasara da karfin gwuiwa.
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamen’e ya jinjina gami da yima sojojin barka da dawowa, kamar yadda kwamandojin sauran bangarorin sojin Iran ma sun fitar da sakonnin barka da dawowa ga sojojin.