Amurka Ta Kai Makamai Da Kayakin Yaki Daga Siriya Zuwa Iraqi.
A jiya talata ce wata tawagar motocin sojojin Amurka daga arewacin kasar Siriya suke shiga kasar Iraqi zuwa sansanin sojojin sama na Amurka take AL-Harir a lardin kurdawan kasar Iraqi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kamfanin dillancin labaran Al-maalumah na kasar Iraqi yana cewa tawagr motocin Amurka dauke da makamai da kuma abinci sun taso ne daga lardin Hasaka na araewacin kasar Siriya wanda kungiyar yan ta’adda ta kasad take iko da shi.
Labarin ya kara da cewa yawan motoci a tawagar sun kai 20 sannan sun sami rakiyar jiragen yaki mawadanda ake sarrafasu daga nesa bayan da tawagar ta shiga kasar Iraqi.
READ MORE : Richado Sa Pinto Ya Zama Sabon Kocin Kungiyar Kwallon Kafa Ta Esteghlal Ta Iran.
Sojojin Amurka suna mamaye da arewacin kasar Siriya tun shekara ta 2014 da sunan yaki da kungiyar Daesh wacce ta kirkiro da kanta. Sannan a halin yanzu tana satar danayen man fetur da suke yankin areawacin kasar zuwa don amfanin kanta da kungiyar yan ta’adda ta kurdawan kasar Siriya KASAD.
READ MORE : Hajji; Alamar hadin kai da hadin kai.
READ MORE : Nakiya ta kashe wani sojin Majalisar Dinkin Duniya a Mali.