Amurka ta ce ta kai hare-hare ta sama kan dakaru da ke goyon bayan Iran a kusa da kan iyakar Iraki da Syria bisa zargin sune suka kai mata hare-hare da jirage marasa matuka kan dakarunta a Iraki.
Wani mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Pentagon ya ce an kai harin ne kan wasu wurare uku da ake ajiyar makamai a yankin.
A kalla sojojin Amerika 2500 ne suke jibge a kasar iraqi bisa yarjejeniyar samar da zaman lafiya da kasashen amurka da iraki suka jima dasanya wa hannu, amma sai dai majalisar dokokin Iraki ta jima da soke wannan yarjejeniya ta kawancen da sojojin Amurka sai dai amurkan taki fita daga Irakin kamar yadda dokar kasa da kasa ta tanadar.
Sanarwar ta ruwaito shugaba Joe Biden na bayyanawa karara cewa Amurka za ta ci gaba da baiwa haramtattun dakarunta kariya da ke yankin.
Kungiyar kare hakkin kai ta ‘yan asalin iraqi ta tabbatar da mutuwar wasu daga cikinmambobin ta a wannan hare-haren jirage marasa matuka sau biyar da aka kaddamar a wuraren ajiyar makaman daga watan Afrilu, baya ga yawan harin rokoki da ake samu a yankin.
Tuni dai gwamnatin Iraqi ta yi tir da wannan hari ta na bayyana hakan a matsayin barazana ga bangaren tsaron kasar
Amerika tace kungiyoyin data kaima hari suna goyon bayan jamhuriyar msusunci ta Iran ne kuma ciki har da ciki har da Kataib Hezbollah.
Kafofin yada labaran Syria sun ruwaito cewa an kashe wani karamin yaro a kusa da iyakar Syria da Iraqi, kuma sun zargi Amerika da neman yin kafar ungulu ga kokarin inganta zaman lafiya a yankunan
Al’ummomi da gwamnatocin kasashen asiya sun gaji da tsomalen Amerika a kasashen su amma abin mamaki amurka ra gaza ta fita daga wadannan kasashen.
Ana sa ran kungiyoyin su dauki fansa a kan kasar ta amerika kamar yadda suka ambata domin cigaba da barin amerikan tana cin karen ta babu babbaka babbar barazana ce ga rayuwar al’ummar yankunan.