Amurka ta gargaɗi Nijar a kan hatsarin aiki da sojojin hayar Rashaac
Amurka ta yi gargaɗi game da hatsarin da ake fuskanta na yiwuwar ƙungiyar sojojin haya na Rasha su yi amfani da juyin mulkin sojoji wajen shiga Nijar.
Sakataren Wajen Amurka, Anthony Blinken ne ya yi wannan gargaɗi lokacin da yake zantawa da BBC, inda ya ce duk inda ƙungiyar sojojin Wagner ta taka, babu abin da take bari a baya sai mace-mace da ɓarnata dukiya da ci da gumin al’umma.
Sojojin Wagner suna aiki a ƙasashe maƙwabtan Nijar.
Shugaban Wagner, Yevgeny Pgozhin dai ya nanata goyon bayansa ga sojojin da suka yi juyin mulki har ma ya ce suna iya kiran sa a duk lokacin da suke so.
Tun da farko mataimakiyar Blinken, Victoria Nuland, ta ce ta gudanar da tattaunawa da sojoji masu juyin mulki a Niamey babban birnin jamhuriyar Nijar kuma ta ce sabbin shugabannin sun fahimci hatsarin yin aiki tare da sojojin Wagner.
Ƙungiyar Raya Ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za ta gudanar da wani taron ƙoli a ranar Alhamis, bayan shugabannin juyin mulkin sun yi biris da wa’adin da ta ba su, na su sauka daga mulki.
Anthony Blinken ya ce babu wani abin alheri da aka taɓa samu a duk inda sojojin hayar Wagner suka sa hannu. Ya ƙara da cewa duk inda Wagner ta je, mutuwa ce take biyo baya, taɓarɓarewar tsaro yana ƙaruwa, maimakon raguwa.
Sakataren wajen ya ce Wagner ba ta taɓa biyan buƙatun ƙasashen da ake magana a kansu ba, idan ana maganar tabbatar tsaro a ɗaukacin ƙasa.
A cewarsa, abin da ya faru, ko yake ci gaba da faruwa a Nijar, ba Rasha ko Wagner ba ne suka haddasa, amma dai sun dage suna ƙoƙarin amfani da damar cin gajiyar haka.
Ya ce sun ga maimaicin abin da ya faru a sauran ƙasashe inda babu abin da sojojin hayar suka tsinana, sai cutarwa, amma ba alheri ba.
Wane ne sabon firaministan Nijar?
Matakin ne zuwa yayin da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, suka yi sabbin naɗe-naɗe ciki har da Ali Mahamane Lamine Zen a matsayin sabon firaminista.
Jami’in, tsohon ministan kuɗi ne kuma a yanzu yana aiki da Bankin Raya ƙasa na Afirka a Chadi.
Ali Mahamane, mutum ne mai shiru-shiru kuma ƙwararren ma’aikaci wanda bai cika shiga harkokin siyasa sosai ba – hakan ne yadda mutane a Nijar suke bayyana sabon firaministan, wanda Majalisar Tsaron Ƙasa ta naɗa. Mai shekara 58, ɗan asalin Zinder ne kuma jami’in kuɗi, sannan ba baƙo ba ne wajen riƙe manyan muƙamai.
Bayan aikin da ya yi a matsayin daraktan majalisar ministoci ga Shugaba Tandja Mahamadou a 2001, a shekara ta 2003 ne ya shiga harkokin gwamnati karon farko a 2003 inda ya riƙe muƙamin ministan kuɗi a gwamnatin Tandja Mahamadou, matsayin da ya riƙe har zuwa watan Fabrairun 2010 lokacin da aka yi wa gwamnatin Tandja juyin mulki.
A watan Yunin 2014 ne kuma aka naɗa shi a matsayin wakilin Bankin Raya Ƙasashe na Afirka a Gabon, bayan a baya ya riƙe irin wannan muƙami a ƙasar Kwatdebuwa.
Gogaggen masanin tattalin arziƙi ne, kuma ya yi fice a kan bin ƙwaƙƙwafinsa wajen kula da harkokin kuɗin gwamnati.
A fagen ƙasashen duniya, Ali Mahamane Lamine Zen ya jagoranci ƙungiyar ministocin kuɗi ta Afirka da Latin har tsawon shekara biyar.
A siyasance, shi ɗan jam’iyyar MNSD Nassara ne, wato jam’iyyar tsohon shugaban Nijar Tandja Mahamadou.
Ya yi karatu a Cibiyar Nazarin Harkokin Kuɗi da Tattalin Arziƙi da Hada-hadar Banki ta Marseille.
Rahotanni daga Yamai, babban birnin Nijar sun ce duk da halin rashin tabbas da rashin sanin inda aka dosa, jama’a masu yawa sun yi murna da sanarwar naɗa Ali Mahamane, matsayin firaminista saboda dattako da ƙwarewarsa.