Amurka ta ce akwai yiwuwar China za ta kai wa Taiwan hari.
Fadar White House ta yi gargadin cewa China na iya kai wa Taiwan hari, matsawar Shugabar Majalisar Amurka Nancy Pelosi ta kai ziyara tsibirin.
Mai magana da yawun fadar John Kirby ya ce hare-haren za su hada da harba makamai masu linzami, ko kuma jibge sojoji a kusa da Taiwan.
A yau Talata ne Ms Pelosi ta sauka Malaysia a ziyarar da take yi nahiyar Asiya.
Kafafen cikin gida a Taiwan da Amurka sun ce tana shirin ziyartar Taipei ranar Talata da daddare, duk da babu sanarwar hakan a hukumance.
Taiwan tsibiri ne mai zaman kansa, to amma har yanzu China na kallon sa a matsayin wani yankinta da ya balle.
Akan haka gwamnati a Beijing ke gargadin Ms Pelosi da kada ta kuskura ta kai ziyara yankin.
READ MORE : Amurka ta sanar da kashe shugaban Al-Qaeda Ayman al-Zawahiri a Afghanistan.
To amma Taiwan ta ce a shirye take ta karbi bakuncin bako ko daga ina ya fito.
READ MORE : Yarima Charles Na Ingila Ya Karbi Rashawa Daga Iyalan Osama Bin Laden.
READ MORE : NDLEA ta ƙwace ƙwayar Tramadol guda miliyan 2.7 a Legas.
READ MORE : Mahara sun kashe mutum bakwai a Filato.