Kasar China ta bayyana cewar Amurka na wasa da wutar da bata sani ba, bayan da shugaban Amurka Joe Biden yayi ikrarin amfani da karfin soji wajen kare Taiwan duk lokacin da ta mamaye ta.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Zhu Fenglian ya bayyana cewar Amurka na kokarin amfani da Taiwan ne domin dakile China, kuma matakin na iya kona ta kurmus.
China ta bukaci Amurka da ta daina wasu kalamai ko kuma daukar wani matakin da suka sabawa yarjejeniyar baya da suka kulla a tsakanin kasashen biyu wanda ka iya haifar da matsala a tsakanin su.
Yayin ganawa da Firaministan Japan Fumio Kashida a Birnin Tokyo, shugaban Amurka Joe Biden yace kasar sa za tayi amfani da karfin soji domin kare Taiwan muddin China ta nemi mamaye ta kamar yadda Rasha ta yiwa Ukraine.
Shugaban yace duk da wannan barazanar da suke yiwa China har yanzu basu sauya matsayin su akan Taiwan da suka amince da shi tsakanin Amurka da China bai sauya ba, amma kuma ba zasu bari a mamaye ta kamar yadda Rasha ta yiwa Ukraine ba.
A wani labarin na da daban kuma wasu ‘yan sama jannatin kasar China uku sun koma doron kasa a wannan Asabar bayan shafe kwanaki 183 a sararin samaniya, lamarin da ya kawo karshen kumbo mafi dadewa a kokarin China na zama jagaba a harkar sararin samaniya.
Maza biyu da mace daya — Zhai Zhigang da Ye Guangfu da kuma Wang Yaping — sun dawo duniya ne da misalin karfe 10 na safe agogon Beijing, bayan da suka shafe watanni shida suna cikin jirgin Tianhe na tashar sararin samaniyar Tiangong na kasar China.