Manyan Jami’an Gwamnatin Amurka sun shirya wani taron kawayen su a kasar Jamus da zummar yadda za’a taimakawa Ukraine da Karin makamai domin kare kanta daga mamayar Rasha, a daidai lokacin da gwamnatin Rashar ke barazanar barkewar yakin duniya.
Bukatar makamai
Makwanni 8 da kaddamar da mamayar wadda ta gamu da suka daga sassan duniya, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya shaidawa Amurka da kawayen ta cewar suna bukatar Karin makamai domin tinkarar abokan gaban su.
Tallafin Amurka
A ziyarar da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da takawaransa na tsaro Lloyd Austin suka kai Ukraine, sun bayyana karawa kasar tallafin Dala miliyan 700 na agaji da kayan soji.
Tallafin Jamus
Kasar Jamus ta kuma sanar da shirin turawa Ukraine karin tankunan yaki, bayan an zarge ta da farko da jan kafa wajen taimakawa kasar.
Masana harkar soji sun ce kasashen yammacin duniya na bukatar taimakawa Ukraine domin dakile hare hare da makamai masu linzami daga Rasha a Gabashin Donbas da zummar korar sojojin Ukraine domin kutsawa da tankunan ta na yaki.
Austin yace burin su shine karya laggon Rasha ta yadda ba zata iya kaiwa wata kasa mamaya ba.
A wani labarin na daban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tur da sabbin hare-haren da Rasha ta kaddamar a yankin gabashin Ukraine, yayin da ya yi kira da a cimma yarjejeniyar kwanaki hudu domin bai wa fararen hula damar ficewa saboda bikin Easter.
Guterres ya koka kan cewa, a maimakon a gudanar da bikin sabuwar rayuwa a wannan lokaci, amma hare-haren na Rasha a gabashin Ukraine sun ci karo da bikin Easter.
Babban Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa manema labarai cewa, wannan yakin na Ukraine ya dada rincabewa tare da karin zubar da jini da lalata wurare sakamakon kaimin da aka kara na farmakin soji.
Guterres ya bukaci a tsagaita musayar wuta saboda alfarmar bikin Easter daga ranar Alhamis zuwa Lahadi, 24 ga wannan wata na Afrilu.
A cewarsa, Easter, lokaci ne na sabonta rayuwa da kuma fata na gari, amma a bana, bikin ya zo cikin wani yanayi na yaki.
Sojojin Ukraine dai sun tabbatar cewa, rikicin ya kazance a yankin gabashin kasar bayan shugaba Volodymyr Zelensky ya ce, Rasha ta kaddamar da gagarumin farmakinta da aka dade ana dako a Donbas.