Bisa sanya idon shugaba Kim Jung Un ne aka yi wannan gwajin, wanda ke alamta cewa kasarsa ta shirya tsaf wajen tinkarar duk wata barazana daga Amurka, a cewar kafar yada labaran kasar ta KCNA.
Makami mai linzamin da Koriyar ta gwada ya nuna alamun zarce duk wanda ta taba yin gwajinsa, kuma zai iya kai farmaki a ko ina cikin Amurka.
A yayin taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a jiya Juma’a, Amurka ta ce gwaje gwajen baya bayan nan tsokana ce mai hatsarin gaske, tana mai kira da a bijiro da wani kudirin da zai tsaurara takunkuman da ke kan Koriya ta Arewa.
A wani labarin na daban kuma Yayin da zaben shekarar 2023 ke kara karatowa a Najeriya, Babbar Jam’iyyar adawar kasar ta PDP na cigaba da fuskantar matsalolin cikin gida inda wasu daga cikin jiga jigan ‘yayan ta ke ficewa suna komawa Jam’iyyar APC mai mulki.
Rahotanni sun ce Ayade ya bayyana sauya shekar ne bayan ganawar da yayi da wasu takwarorin sa a birnin Calabar da suka kunshi shugaban Gwamnonin kasar Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da shugaban Gwamnonin Arewa Simon Lalong da Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma da kuma takwaran san a Jigawa Abubakar Badaru tare da shugaban Jam’iyyar na riko Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe.
Wannan na zuwa ne bayan sauya shekara da Gwamnan Ebonyi David Umahi yayi daga PDP zuwa APC, yayion da takwaran sa na Edo Godwin Obaseki ya bar APC zuwa PDP lokacin da ta hana shi tsayawa takarar wa’adi na biyu.