Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun saka wa Rasha takunkumi.
Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun sanar da ƙaƙaba wa Rasha takunkuman ƙahon zuƙa, a wani martani ga matakin Shugaba Vladimir Putin na amincewa da ‘yancin kan wasu yankuna biyu na gabashin Ukraine da ke karkashin ikon ‘yan aware.
Shugaba Biden ya ce matakan na farko sun hada da na kokarin kassara tattalin arzikin Rasha.
Haka zalika fadar White House ta ce Mista Biden ya fasa ganawa da Shugaba Putin kamar yadda Faransa ta shirya.
Sai dai Rasha ta yi watsi da wannan mataki, daga bisani ma Shugaba Putin ya gabatar da wani jawabi mai kama da bayar da wa’adi ga Ukraine, yana kira ga sojojin kasar su ajiye makamansu.
Ana tsaka da wannan, Shugaban Ukraine Voladmyr Zelensky, ya ce kasarsa ba za ta mayar wa Rasha martanin soji ba, inda ya ce har yanzu akwai damar sasantawa.