Sakataren tsaron amurka lylon austin ya bayyana cewa kasar amurka a shirye take domin fatattakar kungiyoyin ta’addanci, irin su daesh da isis daga kasa afghnanistan, kuma ya tabbatar da cewa amurkan zata tabbatar wadacan kungiyoyi basu iya dawowa kasar ta afghanistan ba domin hakan na iya jefa kasar cikin babbar matsala.
Austin ya bayyana cewa amurkan tana lura sosai da sosai kan abubuwan da suke faruwa a afghanistan din kuma zata tabbatar kungiyoyin na ta’addanci basu sake samun gindin zama a kasar ta afghanistan ba.
Austin dai yana fadan hakan ne jim kasan bayan kammala ziyarar kwnaki a kasashen yankin tekun farisa ranar aljamis.
”Ina ganin al’ummun duniya sun sanya idanu domin su gani Alqaeda zasu iya tattaruwa a afghanistan ko kuma a’a” inji austin.
Sakataren tsaron na amurka ya kara da cewa yanayin Alqaeda shine kokarin sake tattaruwa da samun karfi domin cigaba da ayyukan su na ta’addanci, a somalia ne ko sata asar daba, suna kuma burin tabbatar da cewa babu gwamnati a kasashe dimin tabbabatr da cigaban ayyukan su na ta’addanci, yace ina ganin wannan shine yanayin wannan kungiya.
Wadannan bayanan na austin na zuwa bayan hasashen da dan majalisar dokokin amurka kuma shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar Lindsey Graham yayi na cewa amurka zata koma kasar afghanistan bayan kayen da tasha kuma ta fice a watannin da suka gabata duk da zaman da tayi a aksar na shekaru ashirin ba tare da ta cimma muradan ta ba.
”Lallai zamu koma afghanistan” kamar yadda Lindsey Graham ya bayyana a wata fira da akayi dashi yace lallai dole ne mu koma domin barazanar zata kara girma ne.
Masana lamurran siyasar duniya dai na ganin wannan wani borin kunya ne da amurkan takeyi bayan a karshe ta sha kaye a yakin shekaru ashirin da ta kaddamar a afghanistan din wanda yaci mata miliyoyin daloli da kuma rayukan daruruwan sojojin ta amma ba tare da cimma muradi ba.