America ta shigo da sabbin makamai da kayan aiki zuwa Siriya.
Wani ayarin motocin sojan America ya tsallaka kan iyakar kasar Iraqi inda ya shiga sansanonin kasar da ke arewa maso gabashin Siriya dauke da kayan aiki da makamai.
Wannan ayarin motocin da ke kunshe da manyan motoci 23 dauke da kowane irin makamai da kayan aiki da kayayyaki sun bi ta mashigar Al-Waleed suka nufi lardin Al-Hasakah.
Majiyoyin soji sun shaidawa birnin San’a cewa, isowar ayarin sojojin na da nufin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban sansanonin America a arewa maso gabashin Siriya da nufin tabbatar da satar man kasar ta Siriya.
Wani fashi da makami ne da mayakan Kurdawa da aka fi sani da “Qasd” ke da hannu a ciki.
Yunkurin da America ta yi na daidaita kanta a arewa maso gabashin Siriya na zuwa ne a daidai lokacin da mazauna yankin, da kuma gwamnatin Siriya ke kallon kasancewar a matsayin mamaya.
A wani lokaci da ya gabata, mazauna kauyukan da ke wajen birnin Qamishli sun tilastawa wasu motocin sojojin America uku da suke kokarin tsallakawa kauyen su ja da baya tare da jifan Americawan.
Gwamnatin Damascus ta sha aikewa da kwamitin sulhu da sakatare-general na Majalisar Dinkin Duniya wasiku na yin Allah wadai da kasancewar America a kasar Siriya a matsayin cin zarafin yankinta.
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta yi gargadin yiwuwar kai hare-haren ta’addanci daga wasu kungiyoyi masu dauke da makamai a wasu larduna 4 na kasar Siriya, tana mai cewa halin da ake ciki a gabashin kasar ta Siriya ya zama maras tsaro da tsanani sakamakon ayyukan sojojin America.