Alkaluma sun nuna yadda ambaliyar ruwa ta hallaka mutane kusan 200 a India da Nepal dai dai lokacin da masana ke hasashen yiwuwar sake fuskantar mamakon ruwa a nan gaba.
A Nepal kadai bayanai sun nuna yadda mutum 88 suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ciki har wasu mutum 6 iyalan gida guda da ruwan yayi awon gaba da su.
Masana sun alakanta karuwar ambaliyar ruwan a kudancin Asiya cikin ‘yan shekarun nan da sauyin yanayi baya ga matakan da mutane ke dauka na sare bishiyu.
A yankin Himalayan na arewacin India hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum 55 sanadiyar ambaliyar a Uttarakhand yayin da gidaje da dama suka rushe baya ga katsewar lantarki.
Bayanai sun nuna cewa ambaliyar ta lalata manyan tituna a kasashen biyu.
Wani rahoton kwararru kuma kan muhalli da matsalar sauyin yanayi ya ce adadin mutanen da ambaliyar ruwa ke shafa da kuma wadanda ke cikin hatsarin fuskantar iftila’in a duniya ya karu zuwa kusan kashi 25 cikin 100, a cikin shekaru 20 da suka gabata.
Masanan da suka wallafa wannan rahoto sun ce sun tattara hujjojinsu ne daga bayanan tauraron dan adam da ke nuna samun karin mutane miliyan 86 da a yanzu haka ke zaune a cikin yankuna masu fama da ambaliyar ruwa a sassan duniya.
A halin da ake ciki iftila’in ambaliyar ruwa ke kan gaba tsakanin sauran masifu masu alaka da yanayi wajen addabar muhalli, sakamakon karuwar yawan ruwan sama dake sauka, lamarin da kwararru suka alakanta kai tsaye da matsalar Sauyin Yanayi.
Manyan misalan yadda ambaliyar ruwa ta tagayyara jama’a a baya bayan nan sun hada da abinda ya auku a kasashen Indiya, China, Belgium da kuma Jamus, inda ambaliyar ta lakume rayukan mutane da dama, gami da lalata dukiya mai tarin yawa, mafi akasari a yankunan da marasa karfi ke zaune.
A mafi rinjayen lokuta taswirar da masana ke samarwa kan ambaliyar ruwa na dogaro ne da nauyin ruwan saman da ke sauka da kuma tumbatsar teku da koguna wajen tattara bayanai kan ambaliyar ruwa, sai dai galibi suna gaza samun bayanan kan yankunan da a tarihi ba sa fuskantar iftila’in.
Don cike gibin ne gungun masu bincike na Amurka suka rika bibiyar bayanan tauraron dan adam na hotuna sau biyu a rana dangane da bala’o’in ambaliyan ruwa fiye da 900 da suka auku a kasashe 169 tun daga 2000.
Kawo yanzu Jumilar murabba’in kilomita miliyan 2 da dubu 230 ambaliyan ruwa ta shafa a sassan duniya tsakanin shekarar 2000 zuwa 2018, alamarin da ya rutsa da akalla mutane miliyan 290.