Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afka wa gabar tekun gabashin Afirka ta Kudu ya kai sama da 400, ciki har da mai aikin ceto, kamar yadda wani jami’in yankin ya baiyana, yayin da wasu da dama suka bace.
Daya daga cikin masu aikin lalubo wadanda wannan iftila’in ya rutsa da su ya fuskanci matsalar sarkewar numfanshi wadda sai daukar shi a aka yi cikin gaggawa zuwa asibiti sa’adda daga bisani yace ga garin ku.
Ruwan sama ya fara barkewa a yankin gabashin afirka ta kudun ne da ambaliyar ruwa ya yi kamari, lamarin da ya ba da damar gudanar da bincike da ayyukan agaji bayan da wata guguwa mafi muni da da baza a mace da da’ita ba ta faru a yankin.
Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan birnin Durban ne da ke gabar tekun kudu maso gabashin kasar a farkon makon da ya gabata tare da kashe hanyoyi, da lalata asibitoci da kuma share gidaje da dama.