Maryam Alwan ta gane komai ya zo karshe bayan da ‘yan sandan New York sun kama ta tare da sauran masu zanga-zanga a Jami’ar Columbia, suka loda su a motocin bas tare da tsare su na tsawon awanni.
Amma a yammacin da ya biyo baya, alibar ta jami’a ta samu sakon email daga jami’ar.
An dakatar da Alwan da sauran wasu daliban bayan an kama su a wajen zanga-zangar nuna goyon baya ga Gaza, wata sabuwar dabara da manyan makarantu a Amurka ke amfani da ta don daƙushe zanga-zangar adawa d ayakin da Isra’ila ke yi a Gaza da dalibai ke gudanarwa.
Bukatun daliban sun zama wani bangare na jigon zanga-zangar, inda dalibai da malaman jami’a ke naman da a yi musu afuwa. Abinda ba a sani ba shi ne ko mahukunta za su soke tuhumar sannan kuma shin wannan laifi zai bi su har girman su ko kuwa a’a.
Yanayin dakatar da dalibai yana sauya wa daga wata makarantar zuwa wata.
A Jami’ar Columbia da Kwalejin Barnard dake da alaka da ita, mata, an kama Alwan da gwamman wasu a ranar 18 ga Afrilu, kuma nan da nana aka hana su shiga azuzuwa da ma jami’ar gaba daya, sun gaza zuwa da kan su ko su wakilta wani, haka ma ba sa samun damar zuwa wajen cin abinci na makarantar.
Ana ta tambaya game da makomar karatunsu. Shin z aa ba su damar rubuta jarrabawar karshe? Yaya batun taimakon kudi? Kammala karatu? Columbia ta ce za a samu sakamako bayan kwamitin ladabtarwa ya zauna, amma Alwan ta ce ba a ba ta rana ba.
“Wannan yanayi ne mai bakantawa,” in ji Alwan, dalibar adabi da zamantakewar al’umma.
Abinda ya faro a Columbia ya zama wani takun saka a fadin kasar tsakanin dalibai da jagorori kan nuna adawa da yaki da takaita fadin albarkacin baki.
A kwanaki 10 da suka gabata, an kama daruruwan dalibai, an dakatar da su tare da saka sunayensu a jerin wadanda za a iya kora daga jami’a a wasu wuraren ma an kore su daga makarantun ciki har da Jami’ar Yale, Jami’ar Southern California, Jami’ar Vanderbilt da Jami’ar Minnesota.
Barnard, kwalejin nazarin ‘yanci ta Jami’ar Columbia, ta dakatar da sama da dalibai 50 da aka kama a ranar 18 ga Afrilu tare da korar su ta karfi daga gidajen kwana na jami’ar, kamar yadda daliban suka bayyana a tattaunawar da aka yi da su da jaridar Columbia Spectator, wadda ta samu wasu bayanai na cikin gida.
A ranar Juma’a, Baranard ta sana da sun cimm amatsaya kan ba wa kusan dukkan su damar dawo wa makaranta. Sanarwar da kwalejin ta fitar ba ta bayyana adadin wadanda aka janye wa dakatarwar ba.
A daren da aka yi kamen, dalibar Barnard Maryam Iqbal ta yada wani hoto a shafin X da ke dauke da sakon email da shugaban tsangayarsu ya yi mata yana cewa ta dawo dakinta karkashin kulawar jami’an tsaro kafin a kore ta.
Sakon email din ya ce “Za a ba ki mintuna 15 ki tattara komatsanki da kike bukata.”
Sama da dalibai 100 na Barnard da Columbia ne suka yi tattakin “Goyon Baya a Dalibanmu” a makon da ya gabata inda suka la’anci kama daliban tare da kira da a janye dakatarwar da aka yi musu.
Har yanzu Columbia na kokarin cire antin da aka saka a bayan makaratar inda ake shirin gudanar da taron yaye dalibai a ranar 15 ga watan Mayu.
Daliban na neman jami’ar ta yanke hulda da kamfanonin da ke da alaka da Isra’ila tare da tabbatar da an yi afuwa ga daliban da malaman da aka kama saboda znaga-zanga.
DUBA NAN: Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Bukaci A Tsagaita Wuta
Ana ci gaba da tattaunawa da daliban da ke zanga-zanga, in ji Ben Chang, kakakin Jami’ar Columbia. “Muna da namu bukatun; suna da nasu,” in ji shi.