A Najeriya sama da al’ummomi 100 ne suka tsere daga garuruwansu sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da kuma rikice rikicen addini da kabilanci da ya hada da rikicin manoma da makiyaya a jihar Kaduna.
Da take tabbatar da wadannan alkalumman daga Birnin Gwari, kungiyar tabbatar da ci gaban masarautar Birnin Gwari ta ce a karamar hukumar kawai, akwai kauyuka 60 da ‘yan bindiga suka kori al’ummominsu tun ashekarar 2021.
Shugaban kungiyar, Haruna Salisu, wanda lauya ne, ya ce babu wai mahaluki da ke zaune a wadannan kauyuka, yana mai cewa mutanen yankunan wadanda manoma ne sun bar mahaifarsu ba don sun so ba, amma saboda cin zarafin da ‘yan bindiga ke musu.
A wani labarin na daban A Najeriya an samu mutuwar matane a wani hari da ‘yan bindiga suka kai tareda bude wuta a kan matafiya a kan hanyar Kaduna-Zaria,
Majiyoyi a Najeriya sun ce wannan farmaki ya faru ne a kofar Gayan dake wajen garin na Zaria kuma sun fara aika aikar ce tun misalin Karfe 8 na daren Litinin.
Yan bindigar dai sun kwasi mutane da dama sannan sun harbe wasu da dama kana wasu kuma suka tsere. Hukumomi tareda hadin gwiwar jama’a na kokarin tattance mutanen da ‘yan bindigan suka yi awon gaba da su,yayinda mutanen da suka samu rauni aka garzaya da su asibiti.
Rahotannin baya-baya na nuni cewa,jami’an tsaro sun isa yankin ba tareda bada karin haske ba.