Alummar Moroko Sun Yi Zanga-zangar Goyon Bayan Masallacin Quds.
Rahotanni sun bayyana cewa dubban Alummar kasar Moroko ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ginin majalisar dokokin kasar a birnin Rabat domin nuna goyon bayansu ga masallacin Quds da kuma yin tir da hare-haren da keta huruminsa da sojojin Isra’ila suka yi.
A yan kwanakin nan ne sojojin Isra’ila suka kai hare-hare a yankunan falasdinawa daban daban cikin har da masallacin Quds da hakan yayi sanadiyar shahadar Akalla falasdinawa 17 tare da jikkata daruruwa.
Ana ta bangaren Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Moroko tayi tir da harin da gwamnatin sahayuniya ta kai a masallacin Quds, ta kara da cewa ta na yin Allah wadai da matakin da sojojin Isra’ila suka dauka na keta hurumin masallacin Quds da cin zarafin falasdinawa .
READ MORE : Ana zanga-zanga bayan ɗan siyasa mai ƙyamar musulmi ya ƙona Al Kur’ani a Sweden.
Wannan yana zuwa ne duk da kuduri da hukumar kula da ilimi da aladu da kimiyya da majalisar dinkin duniya ta fitar a shekara ta 2016 ta yi tir da kai hari kan wuraren tarihi ko na Addinin na musulmi ko na yahudawa dake birnin Quds musamman masallacin Quds a matsayinsa na wurin mai tsari da musulmi suke girmamawa.