Alummar Baharain Sun Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Ziyarar Ministan Yakin Isra’ila A kasar.
A jiya juma’a ce dubun dubatan Alummar kasar Baharain suna bazama akan titunan kasar domin zanga-zangar nuna adawa da ziyarar da ministan yaki na Isra’ila Banny Gantz ya kai kasar a boye, inda suka yi tir da gwamnatin Ali khalifa game da dawo da hulda da suka yi da Isra’ila.
Masu zanga-zangar sun rika taka tuturar Isra’ila kuma suna rera taken yin All..wadai da gwamnatin Isra’ila da kuma nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu da ake zalunta,
Ministan yaki na Isra’ila ya isa kasar Bahrain ne a wata ziyara ta farko a irinta da wani jami’in soji na isra’ila yakai wata kasa a yankin tekun fasha , kuma ya samu rakiyar manyan jami’an soji da na tsaro ciki hard a babban hafsan sojin ruwa na isra’ila Admiral David Saar Salama.
Gwamnatin Baharain taki yi wa alummar kasar Karin bayani game da makasudin ziyarar Banny zuwa kasar, domin gujewa zanga-zangar ko nuna rashin amincewar daga alummar kasar.