Shafin jaridar Sadl Balad ya bayar da rahoton cewa, a jiya Allah ya yi wa sheikh Khamis Jabir Saqar babban malamin kur’ani a kasar Masar rasuwa yana da shekaru 68 a duniya.
An haifi shehin malamina shekara ta 1953 a garin Damnahur ad ke cikin gundumar Buhaira a kasar ta Masar.
Ya yi karatu a wajen manyan malamai na lokacinsa, kafin daga bisani kuma ya shiga jami’ar Azhar, inda a cikin kankanin lokaci ya shahara a cikin jami’ar saboda kwazon da Allah ya bashi.
Ya koma ya ci gaba da karantawa a jami’ar Damnahur a bangaren addini, kafin daga bisani kuma ya zama shugaban bangaren bincike kan rubutattun kur’anai a jami’ar Azhar a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007.
Sheikh Jabir Saqar cibiyar azhar ta nada shi a matsayin babban daraktan cibiyar kula da lamurran kur’ani na lardin Buhaira baki daya, kuma ya koma ga Allah ta’ala yana a kan hakan.
A wani labarin na daban Isra’ila ta fara nuna damuwa game da bangado leken asirin da ake zargin kamfanin NSO na kasar da hannu a ciki.
A halin da ake ciki dai Isra’ilar ta kafa wani kwamitin bincike domin bin diddigin lamarin, bisa fargabar kada hakan ya janyo mata rikicin diflomatsiyya.
Ministan tsaron kasar Benny Gantz, ya ce sunan nan suna duba batun.
A kwanan nan ne dai aka bankado labarin leken asirin da ake zargin kamfanin Isra’ila mai leken asiri na NSO da kuma Pegasus.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban kasar Iraki Barham Saleh da na cikin mutane dubu 50 da ake zargin an yi wa leken asiri da manhajar ta Pegasus.
Haramtacciyar kasar isra’ila dai na shan suka gami da kyamata daga bangarori da dama na duniya sakamakon ayyukan saba doka da ka’ida da kasar ta shahara dashi musamman kisan musulmi falasdinawa da korar su daga gidajen su da sojojin na haramtacciyar kasar isra’ila sukeyi, wanda hakan ya kara rura wutar tsanar haramtacciyar kasar isra’ilan musamman a kasashen musulmi da kuma masu rajin kare hakkin dan adam a fadin duniya baki daya.