Aljeriya; Tabbun Ya Ce Alakarsu Na Daram Da Kasar Rasha.
Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya tabbatar da cewa alakar Aljeriya da Rasha ta dade tun shekaru 60 da suka gabata.
Ya kara da cewa, akwai batutuwa da dama da suke tasowa amma dole ne mu tabbatar da matsayinmu da kuma matsayin alakarmu da Rasha, kan cewa alaka ce ta tarihi, wadda ba za ta taba girgiza sakamakon matsin lamba ba.
Ya kara da cewa Rasha kasa ce abokiyar Aljeriya, saboda haka alakarsu na nan daram, kamar yadda kuma alakarsu da Amurka ma tana nan a irin yanayinta.
Tebboune ya jaddada cewa, Aljeriya ba za ta yi watsi da Falasdinu ko yankin Yammacin Sahara ba, domin batutuwa ne na kawar da mulkin mallaka.
Ya ci gaba da cewa, “Algeria kasa ce mai karfi a kungiyar ‘yan-ba-ruwanmu, saboda haka dukkanin matakanta matakai ne da suka dace da kundin tsarin mulki da kuam siyasart ata kasa da kasa.
READ MORE : ‘Yan kasar Canada sun yi kira da a kawo karshen safarar makamai zuwa Isra’ila.
Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bayyana matakin da firaministan kasar Spain ya dauka, na goyon bayan kudirin kasar Morocco kan yammacin Sahara, yana mai cewa, “hakika ba abu ne da ba za a amince da shi ba.