Aljeriya Ta Yi Wa Fursunoni 14,000 Ahuwa Albarkacin Ranar ‘Yanci.
Gwamnatin Ajeriya ta yi fursunoni 14,000 afuwa albarkacin zagayowar ranar cika shekaru 60 da kasar ta samu ‘yancin kai.
A jiya Talata ne kasar Aljeriya ta yi bikinta na cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga turawan Faransa, bayan shafe shakaru na gwabza yaki.
Albarkacin ranar ta 5 ga watan Yuli, gwamnati ta kuma shirya faretin soja na farko cikin shekaru da dama, bayan da shugaban na yanzu Abdelmadjid Tebboune, ya dawo da faretin.
Tsohon shugaban Aljeriyar mirigayi Abdelaziz Bouteflika, ya yi watsi da duk wani fareti na soja.
READ MORE : ‘Yan Siyasa A Sudan Sun Yi Fatali Da Tayin Janar Al-Burhan.
A ranar biyar ga watan Yulin shekara ta 1962 ne Aljeriyar ta samu ‘yancin karkashin jagorancin wani mayakin sunkuru Ahmed Ben Bella, bayan kwashe shekaru takwas ana yakin da ya yi sanadiyyar rayukan mutane akalla 1,500,000.
READ MORE : Amurka; Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum 6 Yayin Faretin Ranar ‘Yancin Kai.
READ MORE : AU Ta Yaba Da Samun Ci Gaban Siyasa A Mali Da Guinea.
READ MORE : Falasdinu; Amurka Na Rufa-rufa Akan Kisan Shireen Abu Akleh.
READ MORE : Burkina Faso; Mutane 34 Ne Suka Rasa Rayukansu A wasu hare-Haren Ta’addaci.