A wani mataki dake tabbatar da kara rincabewar dangartakar diflomasaoyya, Gwamnatin Aljeriya ta haramta jiragen sojan Faransa ketare sararin samaniyarta, biyo bayan takaddamar biza da kuma wasu kalamai da shugaba Emmanuel Macron yayi.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Algeria ta janye jakadanta dake kasar Faransa, Mohammed Antar Daoud sakamakon rashin jituwa dake kara tsananta a tsakanin kasashen biyu.
Kakakin rundunar, Kanal Pascal Ianni, ya shaida wa AFP cewa “sun samu labarin wannan safiyar wannan Lahadi lokacin da suke shirye-shiryen aike da jirage biyu yankin, kwasan sai suka samu labarin haramcin.
To sai dai Lanni ya ce matakin “bai shafi ayyukansu na tara bayanan sirri a yankin Sahel ba.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Algeria ta janye jakadanta dake kasar Faransa, Mohammed Antar Daoud sakamakon rashin jituwa dake kara tsananta a tsakanin kasashen biyu.
Kafin daukar matakin na Aljeriya, shugaban Faransa Eammanuel Macron ya cacaki wata jaridar kasar mai suna Le Monde da ta wallafa labarin cewa Faransar ta yi wa Algeriar Mulkin mallaka cikin Zalunci abin da ya yi wa Algerian zafi.
Kasar faransa dai ta samu matsala da aljeriya ne bayan wasu kalamai da shugaban kasar faransa emmauel macron yayi wanda basuyiwa gwamnatin ta algeriya dadi ba.
Faransan dai kuma ta samu matsala da wasu kasashen turai da suka hada da amurka, ingila da kuma australiya sakamakon wani cinikin nukiliyar jiragen ruwa, a inda matakin da kasashen suka dauka bai yima ita faransan dadi ba, inda ministan harkokin wajen faransan ya kira wannan mataki da ”soka wuka a baya”.
Kasashen turai dai na ta samun matsaloli a cikin gida da waje wanda hakan ake ganin wata ‘yan manuniya ce dake nuna raunin da suke samu a kullum rana.