Kasar Aljeriya, ta sanar da cewa za ta sake duba alakarta da kasar Morocco, bisa zargin Masarautar da hannu a wutar dajin da ke ci gaba da ci a kasar.
mutane da dama ne dai daga ciki har da sojoji suka rasa rayukansu a wutar dajin wacce ta fara ci tun daga ranar tara ga wannan wata na Agusta.
Mahukuntan Algeriya sun sanar da daukan wannan matakin ne yayin wani taron gaggawa na majalisar koli ta tsaron kasar ranar Laraba, wanda shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune, ya halarta.
A cewar sanarwar fadar shugaban kasar, ayyukan kiyaya da Morocco ke aikatawa kan Aljeriya, su ne suka tilasta kwakware alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma tsaurara matakan bincike na tsaro a iyakokin yamma.
Haka kuma gwamnatin Aljeriya, ta zargi wata kungiyar ‘yan a ware ta ‘yan kabilar Kabili dake da zama a birnin Paris, da kuma wata kungiyar mai kishin islama ta Rashad dake da mazauni a birnin Landon da cinna wutar dajin.
A wani labarin na daban kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na farko da ya gudanar a yammacin jiya Talata a birnin Kabul, bayan da mayakan kungiyar ta Taliban suka kwace iko da birnin baki daya.
Kakakin na Taliban ya ce ba su da makiyi a cikin kasar Afghanistan, hatta wadanda suka yi yaki da su, a halin yanzu gaba ta zo karshe, dole ne kowa da kowa ya zo a hada karfi da karfe domin gina kasa.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, sun samu nasarar korar ‘yan mamaya daga kasarsu bayan kwashe tsawon shekaru ana mamaye da kasar, wanda a cewarsa hakan kokarin na dukkanin al’ummar kasar ba kungiyar Taliban kawai ba.
Dangane da ofisoshin kasashen ketare da ke kasar Afghanistan, Zabihullah ya bayyana cewa, za su kare dukkanin ofisoshin jakadanci na dukkanin kasashen ketare da suke a cikin kasar Afghanistan, tare da bayar da kariya ga jami’an diflomasiyya da sauran ‘yan kasashen waje da suke gudanar da ayyukansu a cikin kasar.
Ya ce za su baiwa al’ummar Afghanistan ‘yancinsu ba tare da tauye wa kowa hakkoinsa a matsayinsa na dan kasa ba, kamar yadda kuma za a kafa gwamnati wadda za ta kunshi dukkanin bangarori na al’ummar kasar baki daya, ba tare da mayar da wani bangare saniyar ware ba.